http://www.hausawglwpwzr4svrerazwxt7mqpcw3hfoxp5r7jjrkttqc3qrs5syid.onion/a/magoya-bayan-apc-sun-yi-tattaki-zuwa-ofishin-inec-a-kano/7016570.html
A farkon makon nan hukumar ta INEC ta ayyana dan takarar NNPP, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-gida, a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna a jihar, wanda aka yi a ranar 18 ga watan Maris a Najeriya. Rahotanni sun yi nuni da cewa, yayin tattakin, an ga magoya bayan dan takarar APC, Nasiru Gawuna dauke da kwalaye da aka yi rubutu iri-iri suna waka suna dosar ofishin na INEC.